Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da hawan Daushe a lokacin bikin sallar Eid-el-Kabir da za a gudanar a ranar Asabar.
Sanarwar dakatawar ta fito ne a jawabin da mataimakin sakataren majalisar masarautar jiha, Sule Mamman-Dee ya fitar a ranar Talata. Ya ce an dakatar da bikin ne saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a jihar.
A cewar Mamman-Dee, Sarki, Abdulmumini Kabir-Usman, ya nuna matukar damuwarsa kan matsalar tsaro a sassan masarautar inda ya ce zai halarci Sallar Idi ne kawai a ranar Asabar.
Ya bayyana cewa Sarkin ya shawarci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
