Asiri Ya Tonu: An Kama Jami’an Tsaro Masu Harka Da ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu jami’an tsaro da ke dauke da Naira miliyan 60 da ake zargin ku?in fansa ne na ‘yan bindiga sun shiga hannun hukumomi.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa an kama jami’an tsaron ne bayan da wasu suka fallasa cewa suna dauke da kudin fansa kuma suna kan hanyar kai kudin ne ga ‘yan bindiga barayi daji masu garkuwa da mutane.

Dakarun Sojojin kasa tare da taimakon wasu dakarun sojin sama ne suka kai wani samame a yankin wanda ya sa aka halaka wasu ‘yan fashin daji da kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Wani jami’in tsaro na cikin gida ya shaida wa jaridar PRNigeria cewa “An kwace tsabar Naira miliyan 60 tare da man fetur da wasu bindigogi samfurin AK-47 da wayoyin hannu da kuma harsasai masu yawa.”

Related posts

Leave a Comment