Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jagoran jam’iyyar APC na ?asa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace mataimakin shugaban ?asa, Yemi Osinbajo, ba ?an sa bane ba a siyansace kuma ba ya tare dashi a takarar shugabancin kasa ta 2023.
Tinubu ya yi wannan furucin ne a Abuja yayin zantawa da manema labarai jim ka?an bayan ganawa da gwamnonin APC 12 kan batun takararshi da ya yi.
Taron wanda ya gudana a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, a birnin Abuja, ya zo ne awanni bayan mataimakin shugaban ?asa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana shiga tseren takarar shugabancin kasa.
Da aka tambaye shi me zai ce game da bayyana wa Duniya shiga takarar kujerar shugaban ?asa da Osinbajo ya yi, wanda mutane da dama ke kallonsa a matsayin ?ansa a siyasance, Tinubu ya ce: “Ba ni da wani ?a da ya girma har ya iya ayyana abu mai girma kamar wannan.
