Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar mashahurin Malamin addinin Musulunci Dr Gumi ya fitar da jawabi game da maganganun da akeyi biyo bayan kalaman da yayi akan kisan Deborah Samuel da tayi kalaman batanci da Manzon Allah (S.A.W).
Malamin ya bayyana cewar zagin shugabanni da Malamai shima zagin Manzon Allah ne, ya kamata jama’a su kiyaye. Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a agareshi yace: “Duk wanda yayimun da’a to lalle yayi wa Allah da’a ne. kuma duk wanda ya saba mun ya saba wa Allah ne. Kuma duk wanda yayiwa shugaba da’a lalle yayimun da’ane kuma wanda zai sabawa shugaba to lalle ya saba mun ne”.
Shifa shugaba an sashi ne kawai domin garkuwa dashi ayi jihadi a bayansa ko ayi kariya da shi. Idan yayi umurni da taqwa kuma yayi adalci to lalle yana da wani lada domin haka in kuma ya aikata sabanin haka to yana da zunubi akansa daga gareshi” Al-buhari Da Muslim suka ruwaito daga Abu Hurairah.
1. Yin da’a ga shugabanin da musu biyayya wajibi ne kuma saba musu sabawa Manzon Allah ne koda ko su masu laifi ne ko kuskure, sai dai ayi musu nasiha kawai ba tare da zagi ko batanci ba. Allah – subhanahu wa ta’ala- yayi umurni da musu da’a.
2. Zagin su fasikanci ne kuma zagin wanda yace a mutunta su ne watau Manzon Allah. Kuma Malamai sune magadan annabawa.
3. Ba a yin jihadi sai dai bayan shugaba, amma mutane sun dauki doka a hannunsu wannan sabawa shugabaninne kuma sabawa manzon Allah ne. Ba jihadi bane kisa ne da bijirewa, aikin Alkhawarijawa.
4. Musulunci ba hauka bane, bin tsari ne da biyayya, lalle jama’a su fahimci haka kuma su kiyaye.
5. Saboda haka kai mai zagin Shugabanni da Malamai kasan matsayinka kada Shedan ya rudaka cikin laifi da zunubi. Kame bakin ka ka fadi alheri. Allah Ya gyara muna halayen mu ya ilmantar damu ilimi mai anfani.
