Kasafin Kudi: Najeriya Za Ta Ciyo Bashin Triliyan 11 A 2023 – Ministar Kudi

Ministar Kudi da tsare-tsaren kasafi Hajiya Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin naira Tiriliyan 11 tare da sayar da wasu manyan kadarorin kasar domin samun kudin da za a cike gibin kasafin kudin shekarar 2023.

An ruwaito Ministar na cewa ana sa ran gibin kasafin kudin kasar zai zarta naira tiriliyan 12.42, idan har kasar ta ci gaba ta bayar da tallafin man Fetur a gaba dayan shekarar 2023.

Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ta hallara gaban kwamitin kudi na majalisar wakilan kasar domin gabatar da tsarin kashe kudi na matsakaicin wa’adi na shekarar 2023 zuwa 2025.

Yayin da take bayanin hanyoyin biyu da za a cike gibin ga kwamitin, Ministar ta ce hanya ta farko ta hadar da ci gaba da biyan tallafin man fetur a ilahirin shekarar 2023

Ta ce hanya ta farko an yi hasashen cewa gibin zai kai naira Tiriliyan 12.41 a 2023, idan aka bi wannan hanya gwamnati za ta kashe tiriliyan shida kan tallafin man fetur

Related posts

Leave a Comment