Hukumomi a Turkiyya sun ce sun dakatar da ayyukan ceto a dukkan wuraren da girgizar ?asa ta afku a ?asar, ban da wuri biyu, yayin da ake fargabar ba za a sake ceto wasu da rai ba.
Tun daga safiyar Asabar ba a sake samun wani da rai ba daga ?araguzan gine-ginen da suka rushe.
An ci gaba da aikin neman masu rai a wuraren da lamarin ya fi ?amari na Kahramanmaras da Htay, amma za a tsagaita aikin a can ?in ma a yau Lahadi.
Da yake ziyara a yankin, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, ya sanar da ?arin dala miliyan ?ari na tallafin ?asarsa ga Turkiyya.
“Tun farkon lamarin mun ba da dala miliyan tamanin da biyar don tallfawa da ruwan sha, da abinci, da matsugunai, yau kuma muna sake ba da sanarwar ?arin dala miliyan ?ari don tallafa wa wa?anda suka fi tsananin bu?ata,” a cewar Blinken.
Zuwa yanzu, an yi ?iyasin cewa girgizar da abin da ya biyo baya sun kashe mutum fiye da dubu arba’in da shida a Turkiyya da Syriya.
