Dan takarar shugabancin Najeriya ?arkashin jam’iyyar NNPP Injiya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi mamakin yadda ya ga wasu gwamnonin APC ke zagi ko sukar shugaban ?asar kan sauyin ku?i.
A wani sako da ?an takarar ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce bai ta?a tunanin cewa za a kai matakin da wasu daga cikin gwamnonin za su fito su ri?a zagin shugaba Buhari ba.
‘’Ha?i?a na yi mamakin yadda wa?annan abubuwa suke faruwa, kuma abin sai ya ba ka mamakin me ke damunsu?’’
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce watakila kuma maganar EFCC – cewa wasu daga cikinsu sun ?oye biliyoyin ku?i a gidajensu- haka take.
‘’Dan haka wannan tsari da aka zo da shi, zai mayar da biliyoyin ku?in da suka sace tamkar yayi ko takardu marasa amfani, ina ga wannan shi ne dalilin da ya sa suka fusata’’, in ji Kwankwaso
Ya ?ara da cewa gwamnonin ba suna yi ne don ?aunar talakawansu ba, domin kuwa a cewarsa babu wani dalili ko hujjar da suka nuna cewa suna ?aunar talakawan nasu
