An bayyana cewar babu wani alfanu ko cigaba da talaka a Najeriya ya samu musanman Talakan Arewa a karkashin mulkin Shugaban ?asa Buhari, sai dai tarin matsaloli da wahalar rayuwa kawai.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Talakawan Najeriya Alhaji Imrana Nas, a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a garin Kaduna.
Imrana Nas ya kara da cewar a matsayin Buhari na ?an Arewa ‘yan Arewa sun fi kowa shan azaba a karkashin mulkin shi, hakazalika matsayin shugaban na wanda ya fito daga Jihar Katsina, jihar ta zamo koma baya ta fuskar cigaba kuma ta farko a bangaren matsalar tsaro.
Shugaban Talakawa ya kuma soki lamirin Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina wanda ya fito yana kiran talakawa da su nemi makami domin kare kansu daga ‘yan Bindiga, inda yace wannan maganar banza ce kuma siyasa ce kawai, domin a lokacin da ‘yan sa kai suka bukaci a basu dama domin kare jihar Katsina gwamnan kin amincewa ya yi, sai a yanzu yake surutan banza.
Dangane da kalaman da Garba Shehu mai ba Buhari shawara akan harkar ya?a labarai ya yi na cewar ‘yan adawa ne ke mayar da hannun agogo baya a harkar tsaro domin shafawa Gwamnatin Buhari ba?in fenti, Imrana Nas yace ko ka?an babu gaskiya a wannan magana, gazawa ce ?arara Buhari da mukarraban shi suka samu a gudanar da Mulki.
“A baya ina girmama Garba Shehu a matsayin Jajirtaccen ?an Jarida wanda ke aiki bisa ga gaskiya da kishin jama’a, amma a yanzu na dawo daga rakiyarshi bayan na fahimci Kujerar shi yake karewa kawai”.
