Kaduna: Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Da Dama

Rundunar dakarun Soji ta OPERATION THUNDER STRIKE, tana cigaba da samun nasara a jihar Kaduna, inda suke ragargazar ‘yan bindiga ta jirgin sama a daukan dake jihar.

A ranar 12 ga watan Nuwamban 2020, rundunar sojin saman ta samu nasarar kashe ?aruruwan ‘yan ta’adda, masu dauke da miyagun makamai a wani farmaki da suka ?addamar a sansanin na su.

Dakarun Sojin sun hango ‘yan ta’addan suna tafe a babura tare da shanu da tumaki masu yawa daga kauyen Dankolo suna tunkarar dajin Kwiambana, inda suka yi musu dirar Mikiya kuma suka samu nasarar kashe da dama daga cikin ‘yan ta’adda da suke dauke da miyagun makamai.

‘Yan ta’addan suna tafe ne a babura tare da shanu da tumakai a kauyukan Dankolo da Machitta da ke jihar Kaduna, bayan wata ta’asa da suka aikata a ?auyukan da ke wajen.

Rundunar sojin saman sun hangi ‘yan ta’addan ta wata na’ura mai hangen nesa, inda suka hangi ‘yan ta’addan a kauyen Kaboru, suna tunkarar dajin Kwiambana, nan take suka afka musu da ruwan Bama-bamai suka aike da yawa daga cikin su barzahu.

Kakakin rundunar sojin, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da rundunar rundunar ta fitar, rundunar Operation THUNDER STRIKE ta ragargaji mafi yawan ‘yan bindigan da ke dajin Kwiambana a jihar Kaduna.

Kamar yadda yace, “Ragargazar ta auku ne a ranar 12 ga watan Nuwamba 2020, inda rundunar sojin saman ta samu nasarar kashe daruruwan ‘yan ta’addan da ke dauke da miyagun makamai suna tafe a babura da shanu da tumaki masu yawan gaske, daga kauyen Dankolo suna tunkarar kauyen machitta.”

Related posts

Leave a Comment