Hotunan Kafin Aure Na ?an El Rufa’i Sun Haifar Da Surutai

Bashir El Rufai, ?aya daga cikin ‘ya’yan gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya fitar da hotunan kafin aurensa inda ya nuna wa duniya matar da zai aura.

Bello El-Rufai ya wallafa hotunan kashi biyu a shafinsa na Twitter inda ya yi wa hotunan lakabi da ‘My Nwakaego and I’

Matar da zai aura, Halima Nwakaego Kazaure ita ma ta wallafa hotunansu tare da rubutu na shauki da bada takaitaccen tarihin haduwarsu.

Ta nuna cewa shekaru uku da suka gabata suka fara yi wa juna sako ta kafar dandalin sada zumunta amma yanzu kuma gashi har ana shirin aure.

Ta nuna cewa sahibinta shine kadai mutumin da ke iya jure halayenta duk da cewa wasu lokutan ta kan so sai yadda ta ke so za ayi abubuwa.

Duba da cewa matar da Bashir zai aura tana da sunan Inyamurai ya janyo hankulan ‘yan Najeriya da dama. Wasu sun rika sukarsa don zai auri ‘yar kabilar Ibo duk da kalon da wasu ke yi wa El Rufa’i na ganin kamar ‘yana da matsala da Inyamurai.

Wasu kuma sun ce duk dabara ce ta neman goyon bayan mutanen Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu don siyasar mahaifinsa. Akwai yiwuwar wannan wata dabara ce ta El-Rufai don samun kuri’u daga Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu. El-Rufai ya kware wurin dabara, inji su.

Related posts

Leave a Comment