Arewa Ta Samu Mummunan Koma Baya A Mulkin Buhari – Aisha Yesufu

“Matsalar tsaro ya dade yana addabar arewacin kasar nan ta yadda kullum kashe mutanen yankin arewa akeyi kamar kaji amman munafunci ya hana shuwagabannin yankin arewa magana wurin kawo karshen matsalar.”

“A kowane bangare an bar arewa a baya musamman ta harkar ilimi, siyasa da tattalin arziki duk da yawan jama’ar dake yankin. Mutanen mu basa iya kalubantar gwamnatin shugaba Buhari saboda kawai ya fito daga yankin arewacin kasar nan”.

Kalaman ‘yar gwagwarmaya Aisha Yesufu kenan a cikin shirin “Bakon Mu Na Mako” da gidan Talabijin na Liberty Abuja ke gabartawa, wanda ya gudana a ranar Asabar da ta gabata.

Ni da nafito ina maganar akawo karshen matsalar da ya dami yankin mu amma an samu wasu marasa kishin yankin mu sun fito suna ta la’anta na ciki harda malaman addini Wanda su yakamata ace suna fadawa gwamnati gaskiya amman basa iya yin haka. Akwai wani dan majalisa daya fito yana zagina saboda rashin kishin yankin sa. Kullum sai kaji an kashe mutane amman ko ta’aziya shugaba Buhari baya zuwa yayi balle ya San halin da talakan sa ke ciki.

Mutanen kudancin kasar nan sun fito manyan su da kanana cikin lokaci kadan shugaba Buhari ya dakatar da rundunar SARS. Muda muke da yawan mutane da manya manyan ‘yan siyasa da film din Hausa da mawaka amman mun kasa fitowa mu bayyana wa gwamnatin tarayya matsalar dake damun yankin mu.

Muna da matsala mu kanmu mutanen arewa kuma dole saimun hada kanmu muddin muna son kawo karshen matsalolin da suka addabi yankin mu na arewa. Amman muddin mukasa siyasa, kabilanci da addini a matsalolin mu wallahi bamu da ranar fita daga ciki matsalolin da suke damun arewacin kasar nan.

Kuna goyon bayan ra’ayin Aisha Yuseefu ko kuna da akasin irin fahimtar ta na cewa munafunci yayi wa mutanen mu katutu?

Related posts

Leave a Comment