An Shawarci matasan yankin ?aramar Hukumar Kaduna ta Arewa da jiha baki daya da su dage wajen neman na kansu su rage dogaro da neman aikin gwamnati.
Shawarar ta fito ne daga bakin wani ?an Kasuwa kuma ?an siyasa mai suna Alhaji Abdullahi Ibrahim mai kwai a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a Kaduna.
Mai Kwai wanda ya bayyana Matasa matsayin ?ashin bayan cigaban kowace al’umma, bisa ga haka cigaban su shine cigaban jama’a baki daya.
“Ina son yin amfani da wannan dama in yi kira ga matasa su tuna baiwar da Allah ya yi musu ta hankali da basira, ya kamata su yi amfani da wannan baiwa wajen taimakon kansu da kansu ba jiran wani aiki daga gwamnati ba tun da yanzu aikin gwamnati ya yi wuya, komai kankantar sana’ar ka ka ri?e ta da kyau”.
Daga ?arshe Alhaji Abdullahi Ibrahim mai kwai ya yi kira ga gwamnati da ta ?ara bada dama ga Matasa wajen cire su daga halin kunci da suke ciki.
