Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa wasu al’ummar jihar sun shigar da gwamnati kara gaban kotu inda suke bu?atar a dakatar da gwamnati mai ci da ci gaba da gudanar da ayyukan tsohuwar gwamnatin El Rufai wadanda suka sa?a doka a biranen Zariya, Kafanchan da Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa wani mai suna Mr Yusuf Sule Bobai daga yankin ?aramar Hukumar Zangon Kataf ne ya jagoranci shigar da ?arar.
?arar ta ha?a gwamnatin jihar Kaduna da majalisar dokokin jihar inda aka bukaci su dakatar da duk wani yunkuri na aiwatar da ayyukan tsohuwar gwamnatin saboda cin karo da doka.
?arar ta Yusuf Sule Bobai da gwamnatin jihar Kaduna mai lamba KD/KAD/713/2023 a halin yanzu tana gaban mai Shari’a B. Mohammed na babbar kotun Kaduna.
