Shugaban majalisar tuntu?a ta ?abilar Yarabawa, Afenifere, Cif Ayo Adebanjo ya nemi masu neman takarar shugabancin Najeriya daga yankin kudu maso yamma da su ha?ura.
Shugaban ?ungiyar al’ummar Yarabawa ya ce ya kamata ‘yan takarar yankin nasu kamar Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban ?asa Yemi Osinbajo su bar wa ‘yan ?abilar Igbo don samar da shugaban ?asa na gaba a 2023.
Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wata hira da jaridar Punch ranar Talata, yana mai cewa “rashin adalci ne ?an kudu maso yamma ya zama shugaban ?asa bayan Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya shekara takwas, sannan kuma Yemi Osinbajo zai shekara takwas a mu?amin mataimakin shugaban ?asa”.
