An Bukaci Tambuwal Ya Kafa Dokar Kisa Ga Masu Batanci

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar ya kira taron gaggawa da Malaman masallatan Jumu’a na jihar biyo bayan kashe ?alibar da ta zagi Annabi.

Malaman da suka halarci taron sun shawarci gwamnati a matakin ?asa da jiha ta samar da doka wacce zata haramta ?atanci a kasar nan.

Bayanai sun nuna cewa Malaman sun fito fili sun shaida wa gwamnan cewa matu?ar ba’a samar da doka tare da tsattsauran hukunci ba to jama’a zasu cigaba da ?aukar doka a hannu.

?aya daga cikin Malaman da suka halarci taron ya ce Malamai sun ba da shawara cewa ya dace a kafa doka mai ?auke da hukunci kisa ga duk wanda ya karyata.

A cewarsu, hakan ne ka?ai zai hana mutane yin kalaman ?atanci ga wani addini ko wani Mutum mai daraja a Addini. Hakanan sun shawarci gwamnati ta sanya doka cewa wajibi kowane ?alibi da aka ba gurbin karatu ya yi rantsuwa zai girmama Addinin abokanan karatunsa.

A?alla mutum ?aya ya rasa rayuwarsa yayin da wasu suka jikkata a kokarin jami’an tsaro na kwantar da zanga-zangar da ta ?arke a Sakkwato bayan kashe Debora. Mutane sun fantsama kan tituna a Sakkwato ranar Asabar inda suka nemi hukumomi su sako wa?an da suka kama da zargin kashe wacce ta yi ?atanci ga Annabi (SAW).

Related posts

Leave a Comment