Rahotanni daga masallacin Juma’a na Kakuri dake yankin karamar hukumar kaduna ta kudu na bayyana cewar an kama wani Kirista yayi shigar burtu a sahun Gaba na masallacin a lokacin da ake gudanar da Sallar juma’a.
Mutumin mai suna John Danjuma
Ya saje da Musulmi inda ya shiga sallar juma’a kafin daga baya aka gane shi Kirista ne.
Har kawo yanzu ba a san dalilin hakan ba an mika shi ga kungiyar ‘yan banga na yankin don ci gaba da bincike da daukar mataki.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewar Bawan Allah ya Shiga masallacin yayi Sallah bayan an idar da Sallar Kuma ya cigaba da bara tare da rokon kudi a masallacin.
Jaridar Mikiya
