An kirayi al umma musulmai musammanma mabiya darikar tijjani da su kasance masu hada Kansu waje guda domin samun cigaba dama wanzar da zaman lafiya a kasa baki daya.
Kalifar darikar tijjaniya a Najeriya kuma tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ll ne yayi wnnan kira a wani taro da darikŕr tijjaniya suka shiraya wanda aka gudanar a dakin taro na gidan gwamnati dake yola.
Muhammadu Sanusi yace hadinkai abune da yake da mutukan muhimmanci a tsakanin al umma don haka ya kamata mabiya darikar ta tijjaniya sukasance masu hakuri da kuma mai da hankalin wajen duk abunda zai kawo hadin kai a tsakanin al umma baki daya.
Kalifan ya kuma shawarci al umma da su kara wajen neman sana o in dagoro da kai tare da neman ilimin zamani dana addini wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban addini dama zaman lafiya yadda ya kamata.
Harwayau Muhammadu Sanusi ya kirayi al umma musulmai suje suyi rijistan katin zabe domin su shiga adama da su a harkokin zabe.
Ya kuma shawarci iyaye da sukasance maau tura yaransu zuwa makarantu zamani dana addini wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban ilimi a tsakanin matasa baki daya.
Ya kuma kirayi daukacin al umma musulmai da su cigaba da yin adu o i domin neman taimakon Allah ma daukakin sarki waje kawo karshen sukkanin kalubalen tsaro dake fuskantar kasan nan baki daya.
