Dukiyar Dangote Ta Sake Hawa Sama

Wani sabon rahoton Henley & Partners tare da hadin gwiwar New World Wealth ya ce, dukiyar attajirai a Afrika ta dara $2.4trn, tare da bayyana birane biyar na nahiyar da suka mallaki 50% na dukiyar Afrika.

BusinessInsider ta ce, wadannan biranen sun hada da Johannesborg da Cape Town a Afrika ta Kudu da Alkahira ta Masar da Legas ta Najeriya da kuma Nairobi ta kasar Kenya.

A cewar rahoton, a halin yanzu akwai masu hannu da shuni 138,000 da suke da jarin akalla dala miliyan 1 ko sama da haka, da wasu karin 328 da suka mallaki sama da miliyan 100 na dala ko sama da haka, da masu tarin biliyoyin daloli akalla mutum 23.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya bayyana cewa Afirka ta Kudu na da yawan masu kudi sau biyu fiye da kowace kasa ta Afirka, wanda ya kai kashi 30% na masu akalla $100m a nahiyar. Sai dai kasar Masar ce ke da mafi yawan attajirai a Afirka masu tarin biliyoyin daloli.

Shugaban rukunin kamfanoni masu zaman kansu na Henley & Partners, Dominic Volek, ya ce kasashen Afirka da dama za su fara jan hankalin attajirai ta hanyar ba ‘yan kasa damar zuba jari da zai iya canza tattalin arzikinsu.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, akwai kasashe masu tasowa a Afrika da ka iya fara tashe a fannin kasuwanci, wadanda suka hada da Rwanda, Mauritius da kuma Seychelles, kuma sun fuskancu habakar dukiya da 70%, 69% da 56 cikin shekaru 10.

Ana sa ran Mauritius za ta ga karin attajirai da kaso 75% a cikin shekaru 10 masu zuwa, inda kasar za ta zama mafi saurin habaka a fannin attajirai bayan Vietnam, India da New Zealand. Ana kuma sa ran Namibia za ta shaida karin arzikin attajirai zuwa sama da 60% a cikin shekaru goma masu zuwa, bayan da kwanan nan ta kaddamar da tsarin zama dan kasa ta hanyar saka hannun jari don jawo hankalin attajirai.

Haka nan, ana sa ran yawan attajirai a Afirka zai karu da 42% cikin shekaru goma masu zuwa. Afirka na da wasu kasuwannin da suka fi saurin bunkasa a duniya, wanda hakan ya sa ta zama madakatar attajirai, wanda Dangote ke kan gaba.

Related posts

Leave a Comment