Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce daga safiyar Juma’a ne za a fara kwaso ?aliban ?asar da ke karatu a Sudan bayan sun isa Aswan a cikin ?asar Masar.
Kuma jirgin saman Air Peace da zai yi aikin kwashe ?aliban da sauran ‘yan Najeriya, zai tashi da ?arfe 6 na yamma zuwa Aswan, cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawar.
Mustapha Habib Ahmed ya ce tuni motoci guda biyu ?auke da ?aliban da aka kwaso daga Khartoum suka isa bakin iyaka.
Ya amsa cewa ba shakka sun samu matsala da wasu direbobi da suka zubar da ?alibai a cikin Sahara kusa da Dongola, wani wuri mai nisan kilomita 411 daga Khartum
Mustapha Habib ya ce suna aikin shirya takardu tare da ofishin jakadancin Najeriya a Masar don ganin jirgin Air Peace ya samu damar jigilar ‘yan Najeriyan daga birnin Aswan.
Ya ce tuni suka daidaita da kamfanin sufurin da ya zubar da ?alibai a Sahara, har ma sun shiga motocinsu guda bakwai sun ci gaba da tafiya.
Shugaban na NEMA ya ce motocin bas 13 ne suka fara tashi a ranar Laraba, kuma tuni akwai jami’ansu da ke kan iyakar Sudan da Masar wa?anda ke kar?ar ‘yan Najeriyan da aka kwaso.
