Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin Cire Tallafin Man Fetur

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar kula da tattalin arzi?i ta ?asa ta ce ba yanzu ne lokacin da ya dace a cire tallafin man fetur ba a ?asar.

Ministar Ku?i da tsare-tsare ta ?asar Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan bayan kammala taron Majalisar da aka yi a ranar Alhamis, wanda mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar gwamnati.

Ta ce za a ci gaba da dukkan ayyukan da aka fara game da shirin cire tallafin na tuntubar jihohi da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da wakilan sabuwar gwamnati mai jiran gado.

Zainab ta ce “Majalisar ta amince da cewa dole ne a cire tallafi na farko cikin gaggawa ba tare da wani ?ata lokaci ba, domin kuwa ba abu ne mai ?orewa ba.

“Ba za mu iya ci gaba da biya ba. Dole mu kalli yadda cire tallafin ba zai jefa rayuwar ‘yan Najeriya ba cikin mawuyacin hali.

“Akwai bu?atar neman mafita bayan cire tallafin muna bu?atar yin shiri game da hakan domin tabbatar da an taimaka wa mutane da cire tallafin zai shafa.”

Gwamnatin Najeriya ta ce ta kar?o aron dalar Amurka miliyan 800 daga Bankin Duniya domin sassauta wa mutane ra?a?in cire tallafin.

Related posts

Leave a Comment