Wata mata mai suna Maimuna Wadaji ta cinna wa kanta wuta da zummar kashe kanta da kanta saboda mijinta zai ?ara aure, a cewar ‘yan sandan Jihar Jigawa.
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, ya fa?a wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa matar ta aikata laifin ne a ranar Juma’a da ta gabata a ?auyen Runguma na garin Dutse, babban birnin jihar.
Ya ce Maimuna ta yanke shawarar aikata hakan ne bayan ta samu labarin cewa mijin nata zai sake auren tsohuwar matarsa.
“A ranar Juma’a da misalin 10:00 na safe, ‘yan sanda sun samu labarin wata mai suna Maimuna Wadaji…ta yi yun?urin kashe kanta, inda ta zuba man fetur sannan ta cinna wa kanta wuta,” a cewarsa.
“Daga baya kuma ta yi ihun neman taimako, abin da ya sa aka garzaya da ita asibitin Koyarwa na Jami’ar Dutse (FUD) don yi mata magani.”
