Buhari Ya Yi Rawar Gani Wajen Samar Da Tsaro – Sheikh Jingir

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi magana game da halin rashin tsaro da ake ciki, Malamin yace duk abin da ke faruwa yau, an fuskanci abin da ya fi haka a baya.

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Waikamatis Sunnah ?angaren Jos ya bada shawara, ya yabi shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Malamin yana ganin duk da kalubalen da gwamnatin nan take fuskanta na tsaro, yace Muhammadu Buhari ya zarce sauran shugabannin da suka shude a baya.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana wannan ne a wajen taron gasar Al-Qur’ani ‘musabaqa’ na kasa da aka shirya a garin Gombe. Yace

“Muna fama da manyan matsaloli na rashin tsaro a kasar nan, amma nayi imani cewa halin da ake ciki ya fi yadda ake a baya.” Inji Sheikh Sani Yahaya Jingir.

Related posts

Leave a Comment