Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana farin cikinsa kan yadda ake samun karin mayakan Boko Haram da suke ajiye makamansu su kuma mika kansu ga sojojin da ke jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Babakura Abba-Jato ne ya bayyana hakan a karshen taron da aka yi na harkokin tsaro a ranar Asabar a Maiduguri.
Rundunar sojin Najeriya ta bayar da sanarwar sama da mayakan Boko Haram sun ajiye makamansu tare da duka iyalansu makonni biyu da suka gabata.
Jato gwamnati na farin ciki da wannan ci gaba kuma matsin lambar da sojojin ke yi na daya daga cikin abubuwan da suka haifar da nasarar.
Ya kuma ce shirin komar da ‘yan gudun hijira muhallansu na asali ya kara samar da wani yanayi na jin cewa zaman lafiya na kara samuwa a Borno.Article share tools
