An yi kira jarumai mata da su ke shigowa cikin harkar fim a wannan lokacin da su rinka kiyaye mutuncin su, da kuma sana’ar su, wadda hakan zai sa a rinka kallon harkar da masu yin ta da mutunci.
Jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Hajiya Saratu Gidado wacce a ka fi sani Daso ce, ta bayyana hakan ga wakilin jaridar Dimokuradiyya, a lokacin da su ke tattauna wa, kan lalacewar da masana’antar ta yi a wannan lokacin.
Jarumar ta bayyana cewar “Mu a lokacin da muka shigo harkar nan, a shekara ta 2000, na samu yara irin su Fati Muhammad da su Abinda Muhammad da sauran su, amma ba haka su ke gudanar da rayuwar su ba. Don gaskiya a lokacin da na shiga harkar fim mata yan fim ba sa shaye-shayen kwayoyi kamar yadda yammatan mu na yanzu sabbin shigo wa, a shekarun nan” inji ta.
Ta cigaba da cewar “Duk in da mace take uwa ce, don haka shawara ta duk wadda ta san tana shaye-shaye, duk da ba zan ce wance ba, Amma dai na san ana shaye-shayen don ina ganin alamu sosai, don haka a rinka kame mutunci, domin shaye-shayen da mata su ke yi ya na bata mun rai, kuma ya na damu na sosai. Ni na maza bai dame ni ba, su je can ta matse musu, domin kuwa su maza za su yi aure za su tara iyali. Amma ita ‘ya mace ko ta yi aure ta tara iyali, tarihi ya na nan ba zai goge abin da ta yi ba, ya na nan za a rinka cewar wance ta taba yin shaye-shaye.” Kamar yadda Daso ta bayyana.
Don haka, kada dadin duniya, da rudin kawaye ya sa ku shiga harkar shaye-shaye, don babu mutunci ga kya mace a wajen shaye-shaye. ”
Daso dai Jaruma ce da ta yi suna a fim wajen fitowa a rol din mugunta, wanda tun farkon fitowar ta a fim da wannan rol din ta fara, kuma ta ce, tana jin dadin fitowa a harkar
Jarumar ‘ yar asalin jihar Kano kuma Bahaushiya, an haife ta a 1968, kuma ta yi makarantar firamare da Sakandare, sannan ta yi Diploma a harkar kasuwanci, kuma ta yi koyarwa a makarantar firamare kafin daga baya ta shigo harkar fim, kuma haryanzu ta na cikin harkar fim din, ana dama wa da ita,. Ta na da aure suna zaune da mijin ta a wannan lokacin, don haka auren nata bai hana ta yin harkokin ta na fim ba.
