Bani Da Sha’awar Tsayawa Takarar Siyasa – Malami

Ministan Harkokin Shari’a Abubakar Malami SAN, ya musanta wani rahoto da aketa yadawa na tsayawa takarar Shugabancin Kasa, dashi da tsohon Shugaban Kasar Nigeria Goodluck Ebele Jonathan a zabe mai zuwa na Shekarar 2023.

Mai Taimaka Masa akan Kafafen Yada Labaru Dr Bashir Gwandu, ya bayyana jita-jitar a matsayin hasashen wasu mutane wanda suka kirkira, domin hana ministan gudanar da ayyukan sa na ofis.

Gwandu ya kara dacewa, Malami bai taba tattauna irin wannan al’amarin da kowa ba, kuma bashi da sha’awar tsayawa takara a kowacce kujera, domin aiki yake na yima Kasa hidima iya iyawar sa.

“Akwai sauran lokaci Mai tsawo zuwa shekarar 2023, Kuma bai kamata a fara maganar ta ba, Attoni-Janar bai taba nuna sha’awar tsayawa takara da wani ba.

“Ya kuma shawarci al’umma dasu rika yin tunani akan abunda zasu fada a Kafafen Sadarwa na zamani, ko kuma a kowane wuri.

“Abunda Minista ke bukata a halin yanzu, shine ya maida hankali matuka wajen yin ayyukan da ake bukata a kasar, Kuma tuni shi yake yi, Kuma zai cigaba da hakan”.

Related posts

Leave a Comment