Gwamnatin Kaduna Za Ta Kashe Biliyan 1 Wajen Zamanantar Da KSMC

Gwamnatin jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ta ware kudi Naira bilyan 1 don zamanantar da gidan rediyon mallakarta na KSMC a shekarar badi, 2021.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wasu takardu na yadda za a kashe kudi Naira bilyan 1.4 ga KSMC da aka amince a kasafin kudin 2021 da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya gani.

Takardun sun nuna cewa an ware Naira milyan 45.2 don samar da kayan zamanantar da tashar KSMC a dakin adana wakoki da kuma gyaran gaba daya ga na’urar watsa shirye-shirye ta “transmitter”.

Takardun sun kuma nuna cewa an ware Naira milyan 30 don daga darajar sashen watsa shirye-shirye na Katabu da na babban ofis din KSMC daga KVA 11 zuwa KVA 33.

Kuma an ware Naira milyan 66.2 don zuba kayan aiki a sabon ginin KSMC.

Related posts

Leave a Comment