?ungiyar dattawan arewacin Najeriya, Northern Elders Forum ta ce tana goyon bayan gwamnatin tarayya ta bai wa ?an kabilar Igbo masu fafutukar kafa kasar Biafra damar ?allewa cikin ruwan sanyi, maimakon kisan jama`a ‘Yan Arewa da ?an IPOB ke yi babu gaira babu dalili.
Kakakin Kungiyar Dr Hakeem Baba Ahmed ya ce ?angaren arewacin kasar ya san irin mawuyacin halin da ya shiga a lokacin ya?in basasar da aka yi a baya, don haka yankin ba zai so a sake wani ya?i ba.
“An yi ya?i kowa ya ji jiki. Idan suna son su ?alle kuma shugabanninsu sun goyi bayansu, ba wani dalilin ya?i gara ma su balle domin ya fi zama alheri,” in ji shi
Ya ?ara da cewa babu wani shugaban Igbo da ya fito ya ce abin da suke yi na kashe-kashe da ?one-?one su bari wanda ya nuna a cewarsa, “suna samun goyon bayan shugabanninsu.”
“Fitinar zamansu a Najeriya ta ishemu idan gwamnati ba za ta dauki mataki ba to ta ba su dama a yi ?uri’ar jin ra’ayi .”
