‘Yan Arewa Na Baya Wajen Cin Gajiyar Miliyoyin Kudade Daga Bankin Raya Kasa – Majalisa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin Majalisar Dattawa da ke kula da harkokin bankuna ya yi ?arin bayani kan dalilin da ya sa yankin arewacin Najeriya ba ya samun rancen da bankin raya ?asa yake bayarwa kamar yadda yankin kudu ke samu.

A makon da ya wuce ne Majalisar ta kafa wani kwamiti domin ya gudanar da bincike kan zargin cewa bankin ya mayar da arewa saniyar-ware.

Sanata Ali Ndume ne ya gabatar da ?orafin yayin zaman Majalisar, yana mai cewa daga cikin kusan naira biliyan biyar da bankin ya raba, kashi 11 cikin 100 kacal ya bai wa jihohin Arewa.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC shugaban kwamitin Sanata Uba Sani ya ce rashin bankuna mallakin yankin da ?yamar ku?in ruwa saboda dalili na addini na cikin abubuwan da suka sa yankin Arewa ba ya cin gajiyar rancen sosai.

Uba Sani ya ?ara da cewar sama da kashi 60 cikin 100 na jama’ar Arewa ba su mallaki asusun ajiyar banki ba, sa?anin takwarorinsu na yankin kudu da sama da kashi 80 cikin 100 suke da asusun ajiyar banki.

Shugaban Kwamitin ya kuma koka dangane da yadda yankin arewa ke baya wajen mallakar bankuna, inda ya bayyana cewar dukkanin wani banki da ka gani a kasar nan za ka samu mallakar ‘yan kudu ne.

“A halin da duniya ke ciki yanzu babu yadda za’a yi mutum ya samu wani taimako ko tallafi na ku?i ba tare da ya mallaki asusun ajiyar banki, ashe ya zama dole ga ‘yan arewa su farka daga barcin da suke ciki”.

Related posts

Leave a Comment