IRAN Ta Yanke Wa ‘Yan Madigo Biyu Hukuncin Kisa

Rahotannin dake shigo mana daga ?asar Iran na bayyana cewar wata kungiyar kare hakkin dan adam ta ce an yanke wa masu fafutikar kare ?ancin ?an luwa?i da ma?igo biyu hukuncin kisa a Iran.

Kungiyar mai suna Hengaw ta ce wata kotu ce ta samu Zahra Sediqi Hamedai da Elham Chubdar da laifin ya?a ayyukan ?an luwa?i da Addinin Kirista da kuma tattaunawa da kafafen ya?a labaran da ke adawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

An kuma zargi matan da laifin cin hanci da rashawa wanda hukuncinsa ke zamantowa na kisa a Iran, inda aka sha yanke wa masu fafutika da dama irin hukuncin.

An sanar da matan biyu hukuncin ne a gidan yari inda suke tsare a birnin Urmia.

Related posts

Leave a Comment