Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko babban birnin Jihar Legas na bayyana cewar wani gini mai hawa bakwai da ba a kammala ba ya rushe a birnin inda ya ritsa da mutane da dama.
Rahotanni na cewa ginin, wanda ke kan Titin Oba Idowu Oniru, ya ritsa da mutum kusan shida bayan fa?owarsa a cikin dare wayewar garin Lahadi.
Sakataren hukumar agajin gaggawa reshen Jihar Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce tuni suka ?addamar da aikin ceton wa?anda ginin ya rufe.
“Zuwanmu wurin ke da wuya muka tarar ginin mai hawa bakwai da ba a kammala ba ya rikito,” a cewarsa. “Babu rahoton ko wani ya ji rauni amma ana zaton ?araguzai sun rufe mutum shida.”
Ya ?ara da cewa ma’aikatansu na bu?atar “manyan kayan aiki” a yun?urin ceto mutanen, yana mai cewa sun ?addamar da “shirin aikin ceto na gaggawa na Jihar Legas”.
