Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Zamfara na bayyana cewa wasu gungun ?an bindiga ?auke da muggan makamai sun kashe gwamman mutane a jihar.
?an bindigar wa?anda suka je garuruwan Anka da Bukkuyum a kan babura masu ?umbin yawa, sun afka ?auyukan da ke ?ar?ashin wa?annan garuruwan inda suka rin?a harbi kan mai uwa da wabi tare da cinna wa gidaje wuta.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutanen da ?an bindigan suka kashe sun haura mutum 100. Wani wanda ya shaida lamarin ya shaida wa BBC cewa ya ga gawa ta mutum takwas a wani ?auye.
An bayyana cewa ?an bindigan sun soma kai harin tun daga ranar Talata da dare har zuwa Laraba inda ?an bindigan suka ci gaba da kutsawa daga wanan ?auye zuwa wancan.
