INEC Ta Dage Gudanar Da Zabukan Gwamnoni Da ‘Yan Majalisun Jiha

Hukumar Za?e ta ?asa INEC ta ?age za?en gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da mako guda, wato zuwa 18 ga watan Maris

INEC ta tabbatar wa da BBC ?age za?en, bayan wani taron sirri da manyan jami’an hukumar suka yi a Abuja.

Kafofin ya?a labarai na Najeriya sun ambato cewa INEC ba ta kammala saita na’urar tantance masu za?e ba ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a za?en shugaban ?asa a ranar 25 ga watan Fabirairu.

Sun ?ara da cewa hukumar ta ce sai ta samu damar kwashe bayananta da ta tattara na a yayin za?en shugaban ?asar zuwa wani rumbunta na daban kafin ta sake saita na’urar ta yadda za a yi za?en gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ba tare da wata damuwa ba.

Tun da farko, an tsara gudanar da za?en ne a ranar asabar 11 ga watan Maris.

Wannan na zuwa ne sa’o’i ka?an bayan wata kotun ?aukaka ?ara a Najeriya ta amince da bu?atar hukumar za?e ta ?asar ta sake saita na’urar tantance masu za?e ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a za?en shugaban ?asar.

Tawagar al?alan kotun mai mutum uku ?ar?ashin jagorancin Joseph Ikyegh ta yanke hukuncin cewa an bai wa INEC damar ne domin gudanar da za?en gwamnoni wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 11 ga watan Maris tun da fari.

Hukuncin na nufin kotun ta ?i amincewa da bu?atar da ?an takarar shugaban ?asa a jam’iyyar LP Peter Obi ya shigar ta neman hana INEC goge bayanan masu za?en da aka na?a a za?en shugaban ?asar.

Tawagar al?alan ta ce INEC ta bayyana cewa tana da shirin kwashe bayannan da ke cikin na’urar 176,000 da aka yi amfani da su a za?en ta wallafa su a wani rumbun bayananta na daban, ko da yake Obi da LP ba su nuna ?in amincewa da wannan shiri ba.

Related posts

Leave a Comment