Wasu Daga Cikin Ayyukan Uba Sani A Harkar Ilimi (II)

Daga Ibrahim Ibrahim.

MASU hikimar zance na cewa, da ?an gari akan cin gari. To, Sanata Uba Sani dai kowa ya san cewa jajirtacce ne tun kafin ya tafi Majalisar Dattawa ta 9.

Sanatan ya nuna cewa, lallai shi Haziki ne kuma masoyin Al’ummar da su ka tura shi zuwa kujerar da ya ke a kai yanzu.

A halin da ake ciki yanzu, tun daga lokacin da ya ?are kan kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani ya yi manyan ayyuka na raya al’umma da ci-gaban su.

A yau idan mu ka ?auki fanin ilimi kawai, ana iya cewa Sanata Uba Sani ya kai ?ololuwa wajen inganta harkar ilimi a Jihar Kaduna .

Idan mu ka yi duba da ?angaren ilimin boko da kuma fasaha (ICT), Sanata Uba Sani ya taimaka wajen gina tsangayar koyon Injiniya a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), kan ku?i naira biliyan 3.5, wanda wannan aikin ya kasance babban aikin da wani Dan Majalisa ya taba kawo ma jiharsa a tarihince.

Haka kuma, Malam Uba Sani ya ?auki nauyin karatun ‘yan asalin jihar Kaduna 287 da su ka fito daga manyan makaratun, (KASU), Kwalejin ilimi ta Kafanchan, Kwalejin ilimi ta Tarayya da ke Zaria da makarantar Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria.

Sanata Uba Sani ya gina da sanya kayan aiki na zamani a cibiyar ICT a GSS Kawo da ke a ?aramar Kaduna ta Arewa.

Sanatan ya gina da samar da kayan aiki a cibiyar koyar da sana’o’in hannu da ke a Kinkinau, a ?aramar hukumar Kaduna ta Kudu.

Uba Sani ya gina da samar da kayan aiki a cibiyar ilimin fasahar zamani ta ICT da ke a maza?ar Turunku da ke a ?aramar hukumar Igabi.

Ya gina da samar da kayan aiki a cibiyar koyar da sana’o’in hannu da ke a LEA Sabon Garin Nasarawa, a ?aramar hukumar Chikun.

Malam Uba Sani ya gina ?akunan kwanan ?alibai masu cin gadaje 110 a GGSC Shehu Lawal Giwa da ke a ?aramnar hukumar Giwa.

Ya taimaka wajen gina ?akin kwanan ?alibai mai cin gado 110 a GSS Birnin-Gwari .

Ya gina ajujuwa 6 da ban?aki a LEA ?an Honu 1 da ke a unguwar Millennium City, Kaduna.

Sanatan ya gina ajujuwa 6 a Unguwan Dosa, da ke a ?aramar hukumar Kaduna ta Arewa.

Akwai ayyuka na ci-gaba da dama a game da harkar ilimi da Sanata Uba Sani ya yi a Kaduna ta tsakiya inda ya ke wakilta.

A yau Uba Sani na Sanata ya yi duk wa?annan ayyukan, ina kuma shi ne Gwamnan Jihar Kaduna baki ?aya?

Za?en Uba Sani a matsayin Gwamna alkhairi ne ga jama’ar Jihar Kaduna. Domin kuwa sun gani, kuma duk inda ya je neman ?uri’a cewa ya ke yi bari in fara da fa?in abubuwan da na yi ina Sanata, kafin in fa?i me zan yi idan na zama Gwamna.

Za mu ci gaba…..

Related posts

Leave a Comment