Ina Goyon Bayan Haramta Kiwo A Kudancin Najeriya – Sarkin Fulanin Nasarawa

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ?ungiyar fulani Makiyaya ta miyetti Allah (MACBAN), ta goyi bayan gwamnonin Kudancin Najeriya kan matsayar da suka ?auka na haramta wa fulani makiyaya kiwo a yankinsu domin samar da zaman lafiya a Kudancin Kasar.

Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a Kaduna, jigon Kungiyar Makiyaya MACBAN na ?asa, Sarkin Fulanin Nasarawa Sanata Walid Jibrin, yace wannan matakin zai magance rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Sanatan yace kiwon shanu yakai tsawon sama da shekara 100 ana yinsa a nahiyar Africa ba tare da duba yadda shanun ke yawo ba ko samar musu da matsuguni.

“A wancan lokacin akwai karancin fulani makiyaya, ?arancin manoma da ?arancin shanu shiyasa ba’a duba yiwuwar samar musu da wurin kiwo ba.” “Amma yanzun al’umma sun karu sannan akwai fasahohin noma da kiwo na zamani.”

Sanata Jibrin, wanda shine Sarkin Fulanin Nasarawa, yace bisa damuwar da ake samu kan kiwon shanu a nahiyar Africa musamman Najeriya, akwai bu?atar a duba hanyoyin da za’a inganta shi.

Related posts

Leave a Comment