Buhari Ya Dawo Najeriya Bayan Kammala Taro A Kasar Faransa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar Najeriya bayan tafiyar da yayi domin halartar muhimmin taro a birnin Paris na kasar Faransa, kamar yadda hadimin shugaban kasan Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Shugaban kasan ya iso kasar da misalin karfe 5:15 na yammacin ranar Alhamis inda ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake garin Abuja.

Idan zamu tuna, Buhari ya bar garin Abuja a ranar Lahadi zuwa birnin Paris, inda ya kwashe kwanaki hudu domin halartar gagarumin taron farfado da tattalin arzikin Afrika bayan annobar Korona.

Taron ya mayar da hankali wurin duba tattalin arzikin Afrika bayan girgizashi da annobar Korona tayi, sannan ya samar da sassauci a fannin bashin da suke kan kasashen.

Taron wanda Shugaban kasa Emmanuel Macron na kasar Faransa ya karba bakunci, ya janyo manyan masu ruwa da tsaki na ma’aikatun kudi na duniya da wasu shugabannin gwamnatoci, wadanda suka zauna domin tattauna basussuka da kuma yadda kasashen Afrika zasu samu tallafi na kudi.

Related posts

Leave a Comment