Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar soji tace har yanzun bata samu ingantaccen bayani kan rahoton mutuwar shugaban ?ungiyar Boko Haram, Abubakar She?au ba.
Wani rahoton bincike ya bayyana cewa She?au ya mutu ne a wata fafatawa da suka yi da maya?an dake fafutukar kafa kasar musulunci a nahiyar Afirca (ISWAP).
Rahoton ya bayyana cewa, Abubakar Shekau yaji mummunan rauni yayin da yayi ?o?arin kashe kansa don kada abokan hamayyarsa ISWAP su kama shi a wata fafatawa da suka yi da talatainin daren ranar Laraba.
Wani Rahoton ya kuma bayyana cewa shugaban Boko Haram ?in ya she?a lahira bayan jiwa kansa mummunan rauni, sakamakon harbin kanshi da kanshi da ya yi da Bindiga.
A wata tattaunawa da aka yi da ?wararre a ?angaren tsaro, Kabiru Adamu, yace ko an kashe shakau ko yana raye, ISWAP na ?ara ?arfi idan ka duba irin ayyukan da suke yi a yanzun.
“Abinda wannan rahoton ke nuna wa rundunar soji shine sun bar ISWAP ta ?ara ?arfi a ?angaren kai hare-haren su, kuma wannan mummunan sa?o ne suke aikewa ?ungiyoyin ta’addanci.” “Wannan sa?on na nuna wa mutanen dake shiga rundunar soji da wa?annan ?ungiyoyi cewa gara su shiga wa?annan ?ungiyoyin na ta’addanci saboda sunfi rundunar soji ?arfi.
Da aka tuntu?i daraktan ya?a labarai na rundunar, Brig.-Gen. Bernard Onyeuko, ya fa?awa manema labarai ta hanyar tura sa?o cewa bashi da bayani akan rahoton. “Kuyi hakuri, bani da bayani akan haka.” inji shi.
