Rahoton dake shigo mana daga birnin Ibadan na Jihar Oyo na bayyana cewar wata kungiyar masoya ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, sun bayyana cewa dan takaran nasu zai samu kashi 80 na kuri’un yankin Arewa maso yamma a zaben 2023.
Shugaban kungiyar, Oladosu Oladipo, ya bayyana hakan ne a wani zama da suka yi a Ibadan, jihar Oyo a ranar Alhamis.
Sun bayyana cewa yankin Yarbawa zasu yi duk mai yiwuwa don godewa Tinubu bisa ayyukan kwarai da yayi a matsayin gwamnan Legas da yankin nasu gaba daya.
Sun kara da cewa Tinubu yana da hangen nesa, ilimi, iko da karfin kawo sauyi Najeriya. A jawabinsa, Oladosu yace al’ummar yankin kudu maso yamma sun fahimci cewa yanzu karon Yarbawa su fitar da shgaban kasa, kuma babu bayaraben da ba zai zabi nasa ba.
