Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda, Alhaji Sanusi Buba ta yi nasarar cafke wani matashi, Khamis Abdullahi da ke zaune a NDA Quarters, Kaduna. Wanda ya kware wajen damfara alu’umma da tura masu karaurawar banki ta karya wato alert, inda ya ke shigar sojan sama da sunan K. Abdullahi mai mukamin kaftin.
SP Gambo Isa, jami’in hulda da jama’a na rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, ya bayyana haka a lokacin da ya ke baje-kolin sa ga manema labarai a helkwatar rundunar da ke Katsina. Inda ya ce Khamis ya je wajen wani Mohammed Isah Girka da ke saida motoci a kamfanin Alfra Motors, da ke kan titin IBB cikin garin Katsina, ya gabatar da kansa a matsayin sojan sama, mai mukamin kaftin da ya dawo daga kasar Ingila, da aka turo shi Katsina wani aiki na musamman a matsayin direban jirgin sama. Inda ya nemi sayen wata mota kirar Toyota S, akan kudin har naira miliyan biyar da dubu dari hudu, a wajen inda ake saida motoci. Ya yi alkawarin zai dawo ya biya kudin a ranar 2/12/2020 kuma ranar ya kira wanda zai sayi motar da su hadu a banki First Bank, domin tura mashi kudi, ya tura mashi, ashe alert din bogi ne.
Gambo Isa ya ci gaba da cewa bayan ya tafi, ya kai korafi ga yan sanda, inda aka kamashi a garin Hunkuyi na jihar Kaduna. Tuni dai wanda ake zargin ya amsa laifinsa. Kuma irin Wannan salon ne ya yi amfani da shi wajen damfarar wani mai saida wayar hannu, wanda ya cuci wani Abdulwahab da ke unguwar alkali a cikin garin Katsina, ya amshi wayar dubu dari da tamanin da biyar. An samu motar a hannun sa da riga T-shirt ta sojan sama da mukamin kaftin da bajen majalisar dinkin duniya da wayar hannu da hatimin bankin First Bank da kuma takardar cike kudi ta bankin.
