Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce harin da ‘yan Bindiga suka kai Kwalejin Horas da Sojoji ta NDA dake Kaduna zai sa gwamnatinsa “ta hanzarta ?aukar mataki wajen kawar da ‘yan ta’adda maimakon sanyaya mata gwiwa”.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, Buhari ya mi?a ta’aziyyarsa ga iyalan sojoji biyu da maharan suka kashe ranar Litinin da tsakar dare, yana mai cewa “ba za su rasu a banza ba”.
Wasu rahotanni na cewa maharan sun kutsa makarantar ta horar da sojojin Najeriya na ruwa da na ?asa da na sama a birnin Kaduna bayan sun yi shigar sojoji. Sai dai hukumar kwalejin ta ce sun haura ne ta katangar da ke kewaye da makarantar.
“Ganin cewa harin na zuwa ne a lokacin da sojoji suka matsa wa ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi, shugaban ?asa ya ce wannan mummunan aikin zai jawo hanzarta kawo ?arshen rashin imani kwakwata kuma abin da sojoji ke yun?urin cimmawa kenan cikin ?an?anin lokaci,” a cewar sanarwar.
Sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta ?ara da cewa “maimakon hakan ya sanyaya gwiwar dakarunmu kamar yadda aka tsara, zai ?ara musu azama ne wajen kawo ?arshen miyagu a ?asar nan, a cewar Buhari”.
Wani hoto da ya kara?e shafukan zumunta na nuna gawar sojan da ‘yan bindigar suka sace a harin amma BBC ba ta iya tantance gaskiyar lamarin ba.
