Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar a ranar Talata tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu ya kai ziyara Kaduna don jajanta wa Gwamna Nasir El-Rufai da mutanen jiharsa akan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa a makon da ya gabata.
Tinubu ya samu rakiyar tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashin Shettima, wanda ya sanar da batun bayar da kyautar Naira Miliyan 50 ga wadanda harin jirgin kasan ya rutsa da su.
A cewarsa kowa ya shiga damuwa duba da irin hare-haren da ake kaiwa Jihar Kaduna wanda ya ke janyo halakar daruruwan rayuka da dukiyoyi. Ya kara da cewa ya kamata a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar.
Tinubu ya roki Gwamnan El-Rufai da ya kwantar da hankalinsa ya ci gaba da dagewa wurin yin shugabanci na kwarai.
El-Rufai ya mika godiyarsa ga Tinubu Ya kara da rokon mutanen Najeriya da su bai wa gwamnatin Jihar Kaduna hadin kai wurin kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga.
