Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da za?ukan fitar da ‘yan takara a mu?amai daban-daban a watan Mayun 2022.
Rahotanni sun bayyana cewar jam’iyyar za ta fitar da ?an takarar shugaban ?asa ranar 30 ga watan Mayu.
Za a fara za?uakan ne da na ‘yan majalisar jiha a ranar 17 ga Mayu, yayin da da na ‘yan majalisar wakilai zai biyo baya ranar 19, sai kuma na ‘yan majalisar dattawa ya gudana a ranar 21.
Za?en fitar da ‘yan takara a mu?amin gwamna zai gudana ne ranar 24 ga watan na Mayu.
Bayanai sun nuna cewar ayyana ?an takarar shugaban ?asa da APC za ta yi a watan na Mayu zai kawo karshen turka- turka da ake yi akan wanda Shugaban ?asa Buhari zai mara wa baya a babban zaben dake tafe.
