Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanonin sadarwa sun shiga mawuyacin hali sakamakon datse layukan waya sama da miliyan 72 a kasar a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilun 2022.
A cewar wani kwararre a bangaren sadarwa, umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar zai fi shafar kamfanonin sadarwar ne domin za su yi asarar biliyoyin naira ta sanadiyar hakan.
Kamfanonin sun dogara ne a kan siyar da katin waya don tattara kudaden shiga kuma wannan umurnin babban kalubale ne kai tsaye ga hanyar tattara kudadensu.
An hana kiran waya fita daga layukan da ba a hada da lambobin NIN ba, kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yi umarni.
Masu layukan ba su cike yarjejeniyar wa’adin ranar 31 ga watan Maris da ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zama karkashin Isa Pantami ta diba masu ba. Wata sanarwa daga ma’aikatar ta ce kimanin layukan waya miliyan 125 aka hada da lambobin NIN.
Rahotanni sun bayyana cewa masu layukan na iya hada su da lambobin kafin hukumar NIMC ta toshe su gaba daya. Layukan da aka toshe za su iya amfani da intanet da aika sakonni.
A cewar hukumar sadarwa ta kasa, akwai layuka masu aiki kimanin miliyan 197.77 a Najeriya a watan Fabrairun 2022. Sai dai kuma, datse layukan da aka yi bai shafi aika sakon SMS ba, datar waya da kuma kira masu shigowa, kamar yadda wata majiya a daya daga cikin kamfanonin sadarwar ta tabbatar.
