Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah ta ce hankalin mutanen ta ya matukar tashi kan dokar da Majalisar dokokin jihar Enugu ta zartar na hana kiwo a fadin jihar.
Dokar ta zo bayan yarjejeniyar da gwamnoni kudancin kasar sha bakwai suka cimma, kan cewa daga 1 ga watan Satumbar dokar ta soma aiki.
Miyetti Allah ta ce akwai bukatar masu fada a ji su shigo cikin lamarin domin samun maslaha.
