Shugaban hukumar Zabe ta jihar Kaduna Sararu Audi-Dikko sanar da ?age zaben kananan hukumomi a kananan hukumomi 4 a jihar.
Kananan hukumomin sun ha?a da na Birnin Gwari, Chikun, Kajuru da Zangon Kataf.
Audi-Dikko ta ce annyi haka ne saboda tsananin rashin tsaro da ake fama da shi a wa?annan ?ananan hukumomi.
” Jami’an tsaro da ke aikin samar da tsaro a sun tabbatar min cewa ba zai yiwu a iya gudanar da za?e a wa?annan ?ananan hukumomi ba.
” A dalilin haka ya sa gudanar da zabe a wadannan ba zai yiwu ba. Dole mu ?age zaben saboda tsaron ma’aikatan da mutanen da za su fito za?e da kuma kayan aikin za?e.
Saboda haka hukumar ta ?age zaben zuwa ranar 25 ga wannan wata ta Satumba.
A karshe ta yi kira ga mutane da su fito za?e cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
