Babu Gaskiya A Labarin Za A Rushe Cibiyar ‘Yan Jarida – Shugaban ‘Yan Jaridun Kaduna

Shugaban ?ungiyar ?an jarida reshen jihar Kaduna, Adamu Yusuf ya karyata rahoton da ake ya?awa wai gwamnatin Kaduna za ta rusa ginin ofishin ?ungiyar dake titin Muhammadu Buhari.

” Abinda muka sani shine, gwamnatin Kaduna ?arkashin hukumar raya birane ta jihar, ta aiko mana da takardar cewa lallai mu gyara fasalin shagunan dake kewaye da ginin ofishin mu saboda ya sa?a wa yadda dokar gine-gine.

Yusuf ya ce shine abinda muka sani. ” Babu inda gwamnati ta ce za ta rusa ginin NUJ a Kaduna inda take magana akai shaguna ne kuma tuni mun zauna da su, har kungiyar ta fara ?aukar mataki kafin wa’adin da gwamnatin jihar ta bamu.

Hukumar raya birane na jihar ta aika wa ?ungiyar takardar cewa su gyara fasalin shagunan dake kewaye da ofishin kungiyar wa?anda mallakin kungiyar ne ko kuma ta rusa su ta gyara da kanta.

Wannan takarda ya sa wasu suka rika ya?a rahoton cewa wai gwamnatin jihar za ta rusa ginin NUJ a Kaduna.

Related posts

Leave a Comment