Hukumomin Saudiyya sun sanar da sabbin sauye-sauyen da suka tsara na wannan shekarar tare da sanar da duka hukumomin jin dadin na kasashen duniya.
Wadannan dalilan na cikin wadanda suka kara yawan kudaden hajjin da ake ta kokawa da su.
Sakatare hukumar jin dadin alhazai ta Kano Mohammad Abba-Danbatta na cikin wadanda suka halarci wannan taro kuma ya yi wa BBC karin bayanin kan batun.
Danbatta ya ce a baya ciyar da alhazai da ake yi a Muzdalifah na hannun hukumomin jin dadin alhazai na kasashe amma yanzu ya dawo karkashin kulawar hukumar alhazai ta Saudiyya karkashin Mu’assasa.
