Fitaccen malami Sheikh Kabiru Gombe ya yi kira ga shugaban Kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, su wa Allah su agaza wa maniyyata aikin Hajjin bana.
Sheikh Gombe ya yi wannan kira ne a lokacin Tafsirin Azumi da yake yi a Abuja ranar Litinin.
Fitaccen malamin ya ce amfanin nuna cewa musulmai sun za?i ‘Muslim-Muslim’ ya yi a Najeriya.
” A halin da ake ciki akwai yiwuwar idan ba gwamnati ta saka baki bane wato ta taimaka wa maniyyata ‘ ?an Najeriya ba za su iya zuwa aikin Hajji ba bana.
Hukumar Hajji ta kasa ta sanar cewa nan da kwanaki uku duk wanda bai cika karin naira Miliyan biyu ba kan naira miliyan hudu da ?aori da ya biya a baya ba, to ba zai samu damar yin aikin Hajji ba bana.
Sannan kuma maniyyacin da bai biya Hajjin ba sai yanzu, naira miliyan 8 da ?ori zai biya.
Bisa haka ne shehin malamin ya yi kira da babban murya zuwa ga shugabanni musamman gwamnonin jihohin Arewa su ba mara ?a kunya su cika wa maniyyata karin miliyan biyu da Hukumar Hajji ta bijiro musu da shi da rana tsaka don kada su rasa wannan dama na zuwa aikin Hajji a bana.
” Ina gwamnonin mu na Arewa, Ina Abba Gida-Gida, Ina Ra??a na Katsina, Ina Zulum na Barno, Ina Bago na Neja, Ina Inuwa na Gombe, Ina Uba Sanin Kaduna, Ku wa Allah ku cika wa maniyyatan jihohin ku ku?in Hajjin bana su samu su je su sauke Farali.
