Matsalolin Kasa: Tinubu Ya Soke Bikin Ranar Haihuwarsa

images 2024 03 14T070645.613

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa a yayin da ‘yan Najeriya ke cigaba da fuskantar wahalhalu sakamakon sauye-sauyen manufofin gwamnati, shugaba Bola Tinubu ya soke duk wani nau’i na bikin cikarsa shekaru 72 a duniya.

Shugaba Tinubu a cewar sanarwar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin ya?a labarai, Bayo Onanuga ya fitar, zai cika shekaru 72 a ranar 29 ga watan Maris.

‘Yan Najeriya na cigaba da fuskantar matsaloli da damuwa na rashi tun bayan shelanta janye tallafin mai da shugaban ya yi a farkon wa’adin mulkin sa.

Related posts

Leave a Comment