Buba Galadima, ya soki ?wazon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi a shekaru takwas na mulkin sa.
Galadima, wanda tsohon abokin siyasar Buhari ne, ya kuma yi ikirarin cewa shugaban na Najeriya ya mayar da kasar shekaru 100 baya.
Da ya ke magana yayin wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin ta Arise a ranar Laraba, Galadima ya kuma nuna rashin amincewa da furucin da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya yi, wanda ya yi ikirarin cewa shugaban zai bar Nijeriya mafi kyau kan yadda ya same ta.
Ya ce, “Da ma ya bar kasar kamar yadda ya same ta. Da mun yi masa jinjina har ma da raka shi Daura duk lokacin da ya yi niyyar barin ofis.
“Mutumin ya mayar da Najeriya shekaru 100 baya, ya raba kan ?an Najeriya ta hanyar addini, ya raba Najeriya ta kabilanci, ya durkusar da manufofin tattalin arziki, ya karya dalar da ya same ta a kan Naira 157 yanzu ya bar ta kusan dari takwas, wai idan ma ka same ta kenan.
“a da, rashin tsaro a iya yankin Arewa maso gabas ne kawai sai ?an wasu wurare. amma a yanzu ba za ku iya zuwa ko’ina a Najeriya da idanunku a rufe ba. Dole ne ku kwana kuna addu’a Allah ya kubutar da ku.
“Yanzu idan irin Najeriyar da Femi Adesina ke so kenan, to ina rokon Allah ya bashi irin wahalar da talakawa ke fama da ita a kullum a Najeriya,” in ji shi.
