Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a ranar Juma’a ce Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da Gwamnatin Tarayya kwasar dala miliyan 418 daga asusun jihohi 36 da ?ananan hukumomi 774, da nufin ta biya wasu dillalan gada-gada masu i?irarin cewa sun yi wa jihohi da ?ananan hukumomi ayyukan adadin ku?a?en a shekarun baya.
Dillalan gada-gadar sun ce sun yi wa jihohi da ?ananan hukumomi aikin tuntu?a ne da wasu kwangiloli tsakanin 1995 da 2002, wajen ?o?arin aikin dawo masu da ku?a?en da aka ri?a ?ibar masu ana biyan bashin Paris Club da London Club.
Babban Mai Shari’a Iyan Ekwo ya umarci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da fara kwasar ku?a?en da ta shirya fara kwasa daga watan Nuwamba, har sai bayan an kammala shari’ar da Gwamnonin Najeriya 36 suka shigar a gaban sa.
Gwamnonin 36 sun shigar da ?arar ta hannun gogaggun lauyoyin su biyu, Jibrin Okutedo da Ahmed Raji, wa?anda dukkanin su manyan lauyoyi ne (SAN).
A ?arar da su ka shigar, lauyoyin sun shaida wa kotun cewa Gwamnoni 36 na Najeriya ba su yarda cewa wa?ancan dillalan gada-gadar sun yi ayyukan da su ka ce sun yi a jihohi 36 da ?ananan hukumomi 774 a shekarun baya ba.
Lauyoyin sun ce masu i?irarin sai an biya su ha??in ku?a?en har dala miliyan 418, ‘yan gidoga ne kawai, lamarin babu gaskiya a ciki.
“Kuma idan Gwamnatin Tarayya ta kwashi ku?a?e a asusun jihohi 36, to jihohin za su kasance a talauce, ta yadda biyan albashi ma ba zai yiwu ba.”
Daga cikin wa?anda gwamnoni 36 su ka kai ?ara, har da Ma’aikatar Harkokin Ku?a?e ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Shari’a da Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a da kuma Ofishin Bin-diddigin Ku?a?en Bashi (DMO) da kuma Kwamitin Rabon Ku?a?en Kasa na Gwmnatin Tarayya, wato FAAC.
Cikin watan Agusta ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi biris da shawarar gwamnonin Najeriya, ya rattaba hannun amincewa a biya ‘yan gada-gadar su shida dala miliyan 418, kwatankwacin fiye da Naira biliyan 170.
Hannun da Buhari ya rattaba ne ya sa Ministar Harkokin Ku?a?e ta umarci Ofishin Kula da Basussuka na ?asa (DMO) cewa ya bai wa ‘yan gada-gadar takardun al?awarin biyan su basussukan cikin shekaru 10.
Gwamnonin Najeriya 36 sun rubuta wa Ministar Harkokin Ku?a?e Zainab Ahmed Wasi?a, inda su ka garga?e ta cewa kada fa ta sake ta biya dala miliyan 418 ga ‘yan kwangilar da gwamnonin su ka ce ‘yan gidoga na gidi.
Wasi?ar dai sun rubuta ta ne ta hannun lauyan su Femi Falana, wanda ya rubuta mata hatsarin da ke tattare da biyan ku?a?en.
Falana ya nemi a madadin gwamnonin cewa Minista Zainab ta janye umarnin da ta ba Ofishin Kula da Basussuka (DMO) cewa ya fara shirin bayar da takardun al?awarin biyan ku?a?en a cikin wasu ?ayyadaddun lokuta ga ‘yan kwangilar.
Gwamnonin sun ce ya kamata Minista Zainab ta fahimci cewa sun shigar da ?ara a Kotun ?oli, kuma Kotun ?oli ba ta ce a biya ku?a?en ba, domin har?alla ce da dungu da gidoga kawai.
Ku?a?en wa?anda dala miliyan 418 ne, idan aka canja su zuwa dala a farashin gwamnati na dala 1 Naira 410, za su kama naira biliyan 171 kenan.
Wa?anda za a biya ku?a?en dai su shida sun ha?a da tsohon ?an Majalisar Tarayya Ned Nwoko, wanda ya ke kafa hujja da umarnin biyan wanda Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar a ?arar da su ka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/148/2017.
Sai kuma wasu mutum uku da ke neman a biya su dala miliyan 143,463,577.76 a ?arar da su ka shigar mai lamba FHC/CV/2129/2014.
Su ukun sun ha?a da Riok Nigeria Ltd, Orji Nwafor Orizu da wani mai suna Olaitan Bello.
Akwai kuma kamfanin wani mai suna George Uboh, wanda zai kar?i dala miliyan 47,831,920.
Gwamnonin sun nuna damuwa kan yadda Minista Malami ya ?i jin garga?in zargin har?alla, ya ri?a ?o?arin a biya bashin naira biliyan 159.
An shafe shekaru ba ?aya ba, ba biyu ba, Ministan Shari’a Abubakar Malami na bijire wa garga?in da ake yi masa cewa wasu ku?a?e da ya ke ta ?o?arin ganin an biya daga cikin kason ku?a?en Jihohi da ?ananan Muhumomi har dala milyan 418 (naira biliyan 159), akwai gidoga a cikin lamarin.
Amma duk da garga?in da aka rika yi wa Malami, ciki kuwa har da rahoton da EFCC ta dam?a masa, wanda ta nuna cewa bashin haramtacce ne, ba gaskiya ba ne, shi kuma Minista Malami ya rufe ido sai matsa lamba ya ke yi domin ganin an biya wa?anda aka ce wai su na bin bashin, ta hanyar ri?a cirar kudade ana biyan bashin daga ku?a?en da Gwamnatin Tarayya ke bai wa Johohi da ?ananan Hukumomi a duk ?arshen wata.
Sauran mutane biyun da su ka ha?a kai da Minista Malami domin ganin an biya ku?a?en ido-rufe, sun ha?a da Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da kuma Ministar Harkokin Ku?a?e, Zainab Ahmed.
Batun wannan bashi da ake tankiya da tababar sa, ya samo asali ne daga wani hukuncin da kotu ta yanke cewa wasu ’yan kwangila da jami’an tuntu?a na bin jihohi da ?ananan hukumomi 774 na ?asar nan basussuka.
